Important update: Healthcare facilities
CDC has updated select ways to operate healthcare systems effectively in response to COVID-19 vaccination. Learn more
UPDATE
Given new evidence on the B.1.617.2 (Delta) variant, CDC has updated the guidance for fully vaccinated people. CDC recommends universal indoor masking for all teachers, staff, students, and visitors to K-12 schools, regardless of vaccination status. Children should return to full-time in-person learning in the fall with layered prevention strategies in place.
UPDATE
The White House announced that vaccines will be required for international travelers coming into the United States, with an effective date of November 8, 2021. For purposes of entry into the United States, vaccines accepted will include FDA approved or authorized and WHO Emergency Use Listing vaccines. More information is available here.
UPDATE
Travel requirements to enter the United States are changing, starting November 8, 2021. More information is available here.

Bada Tallafin Ruhaniya da tunanin mutum ga Mutanen da ke da COVID-19 a Gida (Saitunan da ba na Amurka ba)

Bada Tallafin Ruhaniya da tunanin mutum ga Mutanen da ke da COVID-19 a Gida (Saitunan da ba na Amurka ba)

Mutane da yawa da suka kamu da rashin lafiya ko suka rasa wasu ‘yan uwansu suna buƙatan jagoran mallaman addinin su. A yayin annobar COVID-19, mafi aminci hanyar bayar da tallafi na ruhaniya da tunani da halayyar mutum shine ta hanyar waya, bidiyo, ko ta hanyar sadarwar zumunta. Shugabannin ruhaniya na iya yin addu’a, raba wa’azi, da raba saƙonnin bege.

Idan ana buƙatar tallafi na ruhaniya, wannan takaddar tana ba da jagoranci don a yi shi cikin aminci yadda ya kamata.

  • Kiyaye aƙalla tazarar tsawon hannaye 2 (mita 2) daga wasu, gami da lokacin rarraba
    abinci ko addu’a.
  • Sanya abin rufe fuska don hana yaɗuwar COVID-19.
  • Yi la’akari da haɗuwa a waje inda ya fi sauƙi don kiyaye nesantan mutane kuma inda akwai ƙarin iska.

Idan dole ne ku shiga gidan mara lafiya:

  • Wanke hannuwanku kafin shiga da kuma yayin fita daga gidan; don ziyara na tsawan wasu awanni, yawaita wanke hannu yayin cikin gidan.
    • Goge hannu na dakika 20 don cire ƙwayoyin cuta masu cutarwa.
    • Idan ba a samu sabulu da ruwa a sauƙaƙe ba, za ku iya amfani da sabulun hannu wanda ke ɗauke da aƙalla 60% na barasa. Yin hakan zai taimaka wajen hana ku kamuwa ko yaɗa COVID-19 a cikin al’umma.
  • Lokacin da kuke cikin gida, buɗe tagogi da ƙofofi don ba da damar iska ta shiga kuma ta fita.
    • Kada a buɗe tagogi da ƙofofi idan yin hakan na haifar da haɗari ko hatsari ga lafiyar yara ko wasu dangin (misali, haɗarin faɗuwa ko haifar da alamun asma)

Ku samu wasu ‘yan mintuna wajen da wasu da ke cikin gida game da yadda zasu rage haɗarin kamuwa da COVID-19. Faɗa wa mutanen gida cewa wanda da ke da wannan alamomin a cikin gida ya kamata:

  • Keɓe kansu da sauran ‘yan uwa, idan zai yiwu.
  • Idan ba zai yiwu a keɓance daga wasu ba, a bi jagorar gwamnati ga COVID-19, wanda zai haɗa da saka abin rufe fuska ko zuwa cibiyar keɓewar jama’a.

Yayin ziyarar ‘yan uwa:

  • Bayar da kalmomin bege.
  • Zai fi kyau kada a taɓa kowa yayin addu’a a gare su don hana haɗarin kamuwa ko yaɗa COVID-19.
  • Idan ɗan uwan mara lafiya yana fama da matsalar numfashi, ciwon kirji, ko rikicewa, wani ya ƙira lambar wayan da aka ajiye wa matsalolin COVID -19, ya tuntuɓi asibitin da ke kusa, ko kuma kiran motar asibiti.
  • Wanke hannuwanku kafin ku bar gida. Wanke hannuwanku kafin da kuma bayan kun cire abin rufe fuska. Wanke hannuwanku* na tsawon dakika 20 da ruwa da sabulu ko maganin wanke hannu na chlorine, ko kuma amfani da abun wanke hannu da ke dauke da barasa don taimakawa hana kamuwa da COVID-19 ko kuma yaɗa shi a tsakanin al’umma.

Jerin abubuwan da zaku yi ko zaku ɗauka tare da ku kafin ziyartar gidaje

  • Abin rufe fuska
  • Abun saftace hannu da ke ɗauke da aƙalla 60% barasa
  • Kyallen takarda
  • Kayan kulawa na gida: pdf icon[PDF – 693 KB]* Paracetamol, safar hannu na amfani da za a iya yarwa, tsumman wanki, katin ƙira, abun kashe ƙwayoyin cuta, sabulu, abin rufe fuska
  • Jerin bayanan COVID-19 na gida (misali jerin cibiyoyin keɓewa)
  • Jerin sabis na tallafi na zamantakewar al’umma (misali layin wayar salula don addu’a, sadarwar imel, ƙungiyar addu’o’in na hanyar sadarwar zumunta)
  • Jerin ayyukan rigakafin don jaddadawa (duba ƙasa)

Ayyukan da za a ƙarfafa na kiyayewa a lokacin ziyara

  • Kasance a gida lokacin rashin lafiya (sai dai lokacin da kuke buƙatar kulawa ta gaggawa don yanayin rashin lafiya ko kulawar likita)
  • Sanya abin rufe fuska (abin rufe fuska da ba na likita ba ko suturar fuska) idan kun bar gidanku ko kuma idan ba za ku iya keɓe kanku daga wasu ‘yan uwa a gida ba.
  • Rufe tari da atishawa da ƙyalle ko yin amfani da cikin gwiwar hannunku. Jefar da ƙyallen a kwandon shara nan take kuma ku wanke hannuwanku
  • Wanke hannuwanku koyaushe da sabulu da ruwa na aƙalla dakika 20
  • Tsaftacewa da yin amfani da maganin kashe cututtuka a wuraren da ake yawaita taɓawa a cikin gida
  • Iyakance gwargwadon yiwuwar kusanci da wasu a cikin gida waɗanda basu da lafiya ko nuna alamun cutar
    (kiyaye aƙalla tsayin hannu 2 ko mita 2) Duk wanda ba shi da lafiya ko ya kamu da cutar ya kamata ya ware kansa da wasu ta hanyar kasancewa a cikin wani “daƙin marasa lafiya” ko yanki (idan akwai)
  • Kai ne ke da alhakin taimakawa kiyaye lafiyar al’ummarka ta bin matakan rigakafin da aka ba da shawararsu:
    • Ka guji shafar fuskarku da hannuwan da ba a wanke ba, musamman idanunku, hanci, ko bakinku
    • Ku san kuma ku raba gaskiya kawai game da COVID-19 kuma taimakawa hana yaɗuwar jita-jita da ƙyama a cikin al’ummarku

Tuntuɓi hukumomin kiwon lafiya don bayanai da shawarwari kan ayyukan da aka tsara wa al’umma don hanawa da iyakance kamuwa da COVID-19.